BBC navigation

Shugaba Mursi ya yi Allah-wadai da Syria

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:24 GMT
Shugaba Muhammad Mursi

Shugaba Muhammad Mursi na Masar yayin jawabinsa ga taron Kasashe 'Yan-ba-ruwanmu

Shugaban kasar Masar, Muhammad Mursi, ya yi Allah-wadai da gwamnatin Syria, a wani jawabi da ya yi yayin babban taron Kungiyar Kasashe ’Yan-ba-ruwanmu da ake yi a Iran.

A jawabin nasa, Shugaba Mursi ya ce ya zama wajibi a goyi bayan masu adawa da gwamnatin kasar ta Syria, yana mai bayyana gwamnatin Bashar al-Assad da cewa azzaluma ce.

“Juyin juya-halin da aka yi a Masar ranar 25 ga watan Janairu ne kashin bayan juyin juya-halin kasashen Larabawa—abin da ya kai har Tunisia, daga nan ya kai Libya da Yemen yanzu kuma ya karasa Syria”, inji Shugaba Mursi.

Tawagar Syria dai ta fice daga dakin taron lokacin da Mursi ke jawabin—Ministan harkokin wajen Syria, Walid Mouallem, ya bayyana cewa jawabin ka iya rura wutar zubar da jini a Syria.

Jawabin ya kuma fusata mai masaukin baki, wato Iran, wacce babbar kawa ce ga gwamnatin kasar ta Syria.

Ziyarar Shugaban Mursi ce ta farko da wani shugaban kasar Masar ya kai Iran tun bayan juyin juya halin Islama da aka yi a shekarar 1979.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.