BBC navigation

Ryan ya soki gwamnatin Obama

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT

Paul Ryan

Dan takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyar Republican ta Amurka, Paul Ryan, ya caccaki shugaba Barack Obama bisa gazawar gwamnatinsa wajen samar da ayyukan yi.

Mista Ryan ya ce Obama ya gaza yin katabus a bangaren rage bashin da ake bin Amurka, inda ya ce ya kamata kasar ta daina kashe kudaden da a zahiri ba ta da su.

Ryan ya yi wannan tsokaci ne a babban taron jami'yarsu da ake yi a jihar Florida, yana mai cewa idan Amurkawa suka zabe su, za su kirkiro guraben aiki miliyan goma sha biyu a cikin shekaru hudu, sannan su zaftare kudaden da ake kashewa na gwamnati.

Mahalarta taron dai sun kaure da shewa a lokacin da Mista Ryan ya yi musu alkawarin cewa da zarar an zabe su, za su soke shirin kiwon lafiyar da Mr Obama ke aiwatarwa.

Tattalin arzikin Amurka na fuskantar barazana

Mista Ryan ya ce tattalin arzikin Amurka na cikin mummunan yanayi, kuma sake zabar mista Obama zai ta'azzara lamarin.

Ya ce:''A yanzu haka, mutane maza da mata miliyan ashirin da uku suna fafutukar neman aikin yi. Miliyan ashirin da uku ba su da aiki ko kuma suna aikin da bai-taka-kara-ya-karya ba. Mutum guda cikin kowadanne mutane shida a Amurka na cikin talauci. Miliyoyin matasa sun kammala karatu kuma suna son yin amfani da ilimin da Allah ya ba su don ci gaban rayuwarsu, amma rabi daga cikinsu ba za su iya samun aikin da ya dace da fannin da suka karanta ba, ko ma duk wani aiki da ka iya daukar dawainiyarsu''.

Mista Ryan ya ce fatansu shi ne Amurkawa su kasance cikin walwala, sannan tattalin arzikin kasar ya bunkasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.