BBC navigation

Sarauniyar Ingila ta bude gasar nakasassu

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:48 GMT

Sarauniyar Ingila, Elizabeth.

Sarauniya Elizabeth ta bude gasar wasannin nakasassu a birnin London wanda shi ne zai zamo babban al'amari a tarihin gasar wasannin.

An fara bikin ne da wani wasan wuta wanda ke nuna kirkirar duniya da kuma wasu bayanai daga sanannen likitan nan mai cutar laka, Stephen Hawking.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin nakasassu ta Paralympics, Sir Philips Craven, ya ce gasar na da matukar muhimmanci wajen hada kan al'umar duniya.

Ya ce: "Kokarinku (nakasassu) zai karfafa gwiwa kuma zai kayatar da mutanen duniya. Ba wai mutanen da ke wurin nan kawai ba, zai karfafa gwiwar al'ummomi masu zuwa.''

Gasar dai ita ce mafi girma da ake gudanarwa inda 'yan wasa fiye da 4000 daga kasashe 165 za su fafata a fannoni da dama da suka hada da tseren keke da kokawa da kwallon tebur.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.