BBC navigation

Amurka ta rufe bincike game da mutuwar ' 'yan ta'adda'

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:44 GMT

Eric Holder

Ma'aikatar Tsaron Amurka ta rufe binciken da ta ke yi game da tsare mutanen da ake zargi da aikata ta'addanci da Hukumar Leken Asirin kasar ke yi ba tare da tuhumar hukumar da aikata wani laifi ba.

Ma'aikatar ta duba yadda hukumar CIA ta tsare mutane fiye da 100, tare da cikakken bincike game da mutuwar mutane biyu a lokacin da ake tsare da su.

Duk da yake ma'aikatar ba ta bayyana sunayen mutanen ba, rahotanni sun ce mutanen su ne Gul Rahman da Maadel al-Jamadi.

Gul Rahman ya mutu ne a shekarar 2002 a wani gidan yarin sirri mallakin CIA bayan ta daure shi a jikin bango.

Maadel al-Jamadi kuwa ya mutu ne a shekarar 2003 a gidan yarin Abu Ghraib da ke Iraqi.

Gwajin da aka yi a kan gawarsa ya nuna cewa kashe shi aka yi.

Babban Lauyan gwamnatin Amurkar, Eric Holder , ya ce an rufe binciken da ake yi game da mutuwar mutanen saboda babu wata cikakkiyar shaida da ta nuna cewa kashe su aka yi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi Alla-wadai da matakin da ma'aikatar tsaron Amurkan ta dauka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.