BBC navigation

Amurka za ta kai karar marubucin littafin Bin Laden

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 05:13 GMT

Osama Bin Laden

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce tana shirin gurfanar da marubucin littafin da ya yi bayani dalla-dalla a kan yadda aka kashe Osama Bin Laden a bara gaban kotu.

A wata wasika da ta aikewa tsohon Babban Hafsan mayakan ruwanta, wanda ya rubuta littafi maisuna "No Easy Day" a turance, ma'aikatar tsaron Amurka ta ce abin da marubucin ya yi ya sabawa yarjejeniyar rashin fitar da bayanan sirrin da ya kulla.

Tsohon Babban Hafsan mayakan ruwan na cikin dakarun Amurka da suka kai harin da ya yi sanadiyar kashe Osama Bin Laden a kasar Pakistan.

Marubucin littafin dai ya boye sunansa inda ya yi amfani da sunan Mark Owen.

Mark Owen dai ya rubuta littafi ne a kan yadda suka kai samamen da ya yi sanadiyar kashe Osama Bin Laden ba tare da samun umarni daga ma'aikatar tsaron Amurka ba.

Babban Lauyan ma'aikatar, Jeh Johnson, ya ce sun yi nazarin littafin inda suka gano cewa Mista Owen ya sabawa yarjejeniyoyin adana sirri wadanda ya amince da su fiye da shekaru biyar da suka gabata.

Kazalika, Mista Johnson ya gargadi kamfanin da ya wallafi littafin mai suna, Penguin Putnam, da ya dakatar da sayar da littafin, musamman wanda za a fitar a makon gobe, yana mai cewa yin hakan zai kara cakuda halin da ake ciki.

Ya kammala gargadin da cewa ma'aikatar tsaron Amurka na shirin daukar matakan shari'a a kan Mista Owen da ma wadanda ke aikin wallafa littafin tare da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.