BBC navigation

Ana gudanar da zabe a Angola

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:45 GMT

Magoya bayan jam'iyar MPLA

A ranar Juma'a ne al'ummar kasar Angola suke kada kuria'unsu a zaben mambobin majalisun dokokin kasar.

Wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali tun bayan wani yakin basasa da aka dade ana yi a kasar.

Jam'iyyun siyasa tara ne za su nemi kujerun 'yan majalisun dokoki, kuma jam'iyyar MPLA mai mulki wacce ta samu yawan kujeru 80 a shekara ta 2008, ita ce ake kyautata zaton za ta lashe kujerun 'yan majalisun dokokin, amma fa ba tare da wata tazara mai yawa ba.

Angola dai ita ce kasa ta biyu mafi karfin arzikin man fetur a Afirka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.