BBC navigation

Gubar dalma ba ta kashe kowa a Zamfara ba - Gwamnatin Zamfara

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:16 GMT

Wata mahaka zinare a Najeriya

Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya ta karya ta rahotannin da suka ce akalla yara biyu sun mutu sakamakon ta'ammuli da gubar dalma.

Kazalika, gwamnatin ta musanta maganar da ake cewa an samu burbushin gubar dalma a wasu kananan hukumomi guda hudu na jihar da suka hada da Samaru, Tsunami, Polo a karamar hukumar Gusau, da kuma Maitsoshi a Magami.

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Ibrahim Mohammed Birnin Magaji, ya shaida wa BBC cewa, '' Ko 'yan jaridar da suka dauki labarin sun je asibitin da aka ce an kai mutanen da suka mutu, likitoci sun tabbatar musu cewa ba gaskiya ba ne. Shugaban Karamar Hukumar Gusau, da Kwamishinan Lafiya, da ma'aikatan Ma'aikatar Muhalli sun nuna cewa wannan abu ba gaskiya ba ne. Don haka muna nan a kan wannan matsayi cewa ba gaskiya ba ne''.

Ibrahim Mohammed Birnin Magaji ya ce a baya su ne suka bayyanawa duniya cewa Jihar na fama da matsalar gubar dalma, don haka ba za su boye komai ba da a ce a wannan karon ma an samu matsalar.

Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Mohammed Kabir Danbaba, shi ne ya sanar da mutuwar yara biyu sakamakon ta'ammuli da gubar dalma a gidan rediyon Jihar ta Zamfara, bayan da binciken wadansu kwararrun likitoci ya tabbatar da cewa yaran biyu sun mutu ne sanadiyyar kamuwa da cutar gubar dalmar.

A shekarar 2010 daruruwn yara sun mutu a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke Jihar ta Zamfara sanadiyar taammali da gubar ta dalma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.