BBC navigation

Angola: an soma samun sakamakon zabe

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:03 GMT

Takardar kada kuri'a

Sakamakon da ya soma fitowa daga zaben kasa baki daya Angola na nuna cewa, jam'iyyar MPLA mai mulki, tana kan gaba, amma kasa da irin yawan kuri'un da ta samu a zaben da ya gabata.

Idan har hakan ta tabbat, to wannan na nufin Shugaba mai ci, Jose Eduardo dos Santos, wanda ya shafe fiye da shekaru talatin akan karagar mulki, zai samu wani sabon wa'adin mulkin.

Sai dai kuma an bara rahoton rashin fitowar jama'a a rumfunan zabe.

An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a mafi yawan wurare, duk da cewa, anyi koken aikata magudi a wasu wuraren.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.