BBC navigation

Mutane akalla talatin sun mutu a Guinea

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:47 GMT
Shugaba Alpha Conde na Guinea

Shugaba Alpha Conde na Guinea

Jami'an gwamnatin Guinea sun ce akalla mutum talatin sun mutu yayin wani hadarin jirgin ruwa a tekun Atlantika.

Jirgin ruwan, wanda ya taso daga birnin Conakry za shi tsuburin Kassa, ya nutse a teku ne sakamokon iska da ruwa mai karfin gaske.

Daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu, Mame Asta Bangoura, ta bayyana cewa:

“An yi ta iska mai karfin gaske, sai kuma injin din jirgin ya dauke wuta, amma aka ta da shi, sannan kuma ya sake mutuwa, kuma daga nan ne jirgin ya fara nutsewa”.

Irin wannan hadari dai ba wani sabon abu ba ne a Guinea da ma wadansu kasashen Afirka saboda yadda ake yiwa jiragen ruwa lodin da ya wuce ka'ida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.