BBC navigation

Tsohon Archbishop na Milan ya soki Cocin Katolika

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Gawar Cardinal Carlo Maria Martini

Gawar Cardinal Carlo Maria Martini

Kwana guda bayan mutuwar tsohon Archbishop na Milan kuma fitaccen malamin littafin Baibul, wata jarida da ake bugawa a birnin mai suna Corriere Della Sera ta wallafa wata hira da aka yi da Cardinal Carlo Maria Martini.

A cikin hirar, malamin na addinin Kirista wanda ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a yana da shekaru tamanin da biyar a duniya, ya yi kakkausar suka a kan Cocin Darikar Katolika.

Dubban mutane ne dai da suka yi jerin gwano suka kuma kwashe sa'o'i suna wucewa ta gaban gawar Cardinal Martini a babbar majami'ar birnin Milan, wadda a cikinta za a binne shi ranar Litinin.

Cardinal Martini mutum ne wanda ba ya shakkar fadin abin da ke zuciyarsa a shekaru ashirin da biyun da ya yi yana jagorantar daya daga cikin tarurrukan mabiya Darikar Katolika mafiya girma a Turai.

A shekara ta 2002 ya kamu da cutar Parkinson's mai lahanta laka, al'amarin da ya sa ya yi murabus ya koma birnin Kudus.

Hirarsa ta karshe

A hirar tasa ta karshe, wadda ya yi kasa da wata guda da ya gabata, Cardinal din ya ce Cocin bay a tafiya da zamani kuma tunaninsa na shekaru dari biyu da suka gabata ne; sannan kuma mabiya Darikar Katolika ba su da kwarin gwiwa a kan Cocin nasu.

Ya kuma ce Cocin ya gajiya, ta'adunsa sun tsufa, majami'unsa na da girma amma fayau suke, yayin da shugabanninsa ke kara nisa da jama'a, sannan abayoyin da malamansa ke sanyawa suka zama na kawa da dagawa.

Cardinal din ya yi kira ga Cocin na Katolika ya amsa kurakuransa, sannan ya fara daukar muhimman matakan kawo sauyi—ya kuma fara sauyin daga kan Paparoma da bishop-bishop din da ke tare da shi.

Ya kuma ce matukar Cocin bai sassauta matsayinsa dangane da wadanda aurensu ya mutu ba, to zai rasa biyayyar al'ummu na baya.

Cardinal Martini ya kuma goyi baya a yi amfani da kwaroron roba—abin da ya ce wani abu ne baiki-baki wanda ya fi baki kirin.

Shekaru goma da suka wuce Cardinal Martini na cikin wadanda ake ganin suna da kyakkyawar damar darewa kujerar Paparoma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.