BBC navigation

Musulmi da Kirista a Najeriya sun yi taro a Bauchi

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:36 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

An gudanar da wani taro tsakanin Musulmi da Kirista a garin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda masana suka gabatar da kasidu a kan yanayin zamantakewa.

Taron dai wani yunkuri ne na dinke baraka tsakanin al’ummomi, musamman mabiya addinai mabambanta—barakar da yanzu haka ke zama wani babban kaluble ga wanzuwar kasar.

Kungiyar Matasa Musulmi ta Nijeriya, wato NACOMYO, ita ce ta shirya wannan taro da nufin fadakar da Musulmi da Kirista game da bukatar fahimtar juna da kuma wanzar da zaman lafiya ta hanyar yin la’akari da yawan tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin mabiya addinai mabambanta.

Wani babban jami’I na kungiyar a jihar Bauchi, Malam Muhammad Rabiu Muhmmad, ya shaida wa wakilin BBC cewa:

“Mun dubu irin halin da kasarmu take ciki—musamman arewa—na rashin yarda da abokan zamanmu wadanda ba Musulmi ba da kuma kabilu daban-daban, shi ya sa muka gay a kamata mu shirya wannan taro mu kuma kira jama’a a zo a fadi yadda da zamanmu yake, da kuma menene yake jawo mana matsala yanzu, mu ga yadda za a warware saboda a koma a zauna kamar yadda ake da”.

'Siyasa ce ta kawo matsala'

Taron dai ya gayyato matasa ne daga bangarorin addinai wadanda galibi ake zargi da bari wadansu manya na amfani da su don haddasa fitina.

Sai dai kuma a ganin jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Matasa ta Adddinin Kirista a Jihar Bauchi, Adamu Jonathan Sambo, siyasa ce ta shigo da rigingimu a Najeriya domin a da can Musulmi da Kirista na zaune lafiya a kasar.

“Daga baya siyasa ta zo ta haddasa mana matsalar da muke fama da ita a yau; kuma siyasa, saboda ta cuce mu, ta saka addini amma ba addinin ne siyasa take daukakawa ba”.

Taron dai ya fi mayar da hankali ne a kan yadda matsalar rashin tsaro da lalacewar zamantakewa a arewcin Najeriya ke dada muni.

Inda matsalar take

Barista Solomon Dalung na cikin wadanda suka gabatar da makaloli a taron, ya kuma bayyana cewa:

“Arewa dai ta samu kanta cikin tsaka mai wuya domin rigingimu da kuma rashin shugabanci.... Abin da ake yi shi ne ana kiran wadanda ke da manja a hannunsu, sai a ba su farar riga su saka, amma sauyin da aka samu yanzu shi ne na tara matasa ne wadanda ake yiwa kallon shugabannin gobe [na shaida musu] cewa idan suka yi wasa to gaba akwai matsala”.

Shi ma Dokta Bawa Abdullahi Wase, wani babban mai bincike a kan tsaron bil-Adama a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ya gabatar da kasida.

“Na shaida musu a duk abubuwan da suke hannunmu, babu wani abu da ya taba nunawa cewa da Musulmi da Kirista ba su da fahimtar juna a Najeriya. Mugayen shugabanni kalilan ne suke wannan domin su wawushe dukiyar al’umma”, inji Dokta Wase.

To sai dai kuma wani abin damuwa a cewar masu lura da al’amura shi ne yadda aka sha gudanar da tarurruka da kuma bayar da shawarwari a kan yadda za a samar da zaman lafiya a Najeriya, amma kuma ba kasafai ake ganin tasirin irin wadannan matakai, ko da yake dai masu hikimar magana na cewa mai rai ba ya fitar da tsammani da alheri.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.