BBC navigation

An dakile hari kan kwalejin sojin sama a Syria

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:14 GMT
'Yan tawayen Syria

'Yan tawayen Syria

Gwamnatin Syria ta ce ta dakile wani gagarumin hari da ’yan tawaye suka kai a kan wata kwalejin horar da sojin sama da ke kusa da birnin Aleppo a arewacin kasar.

Babban labarin da gidan talabijin na kasar ya yi ta yadawa shi ne dakarun ’yan tawaye sun kai hari a kan kwalejin ta Rasm al-Abboud.

Gidan talabijin din ya nuna motoci da dama dauke da bindigogi masu sarrafa kansu da sauran makamai, wadanda ya ce an kwace lokacin da aka dakile harin.

Kwalejin dai daya ce daga cikin sansanonin sojin saman da suka fuskanci hare-hare a ’yan kwanakin nan, yayinda mayakan ’yan tawaye ke kokarin kawo karshen yawan amfani da gwamnati ke yi da jiragen sama masu saukar ungulu wajen tallafawa dakarunta na kasa.

Babu alamun sassauci

Gidan talabijin din ya kuma bayar da rahoton wadansu jerin nasarori a kan abin da ya kira ’yan ta'adda masu dauke da makamai a sauran wurare.

Sai dai babu alamun cewa dakarun gwamnatin sun dauki hanyar yin nasarar karbe birnin na Aleppo wanda shi ne birni mafi girma a kasar.

A bangare daya kuma, sabon wakilin kasashen duniya mai shiga tsakani a kasar ta Syria, Lakhdar Brahimi, ya karbi aiki a hukumance daga Kofi Annan.

Mista Brahimi dai kwararre ne a harkar diflomasiyya, sai dai kuma ya yi gargadin cewa babu wani lakani wanda kwaf daya zai iya kawo karshen rikicin da ake yi, kasancewar alamu na nuna cewa daga gwamnati har ’yan adawa babu mai nuna alamaun sassauci.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.