BBC navigation

Kamfanin Gruenenthal ya nemi afuwa daga wadanda suka nakasa

An sabunta: 1 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:01 GMT
Mata a asibiti

Mata a asibiti

A karon farko cikin shekaru hamsin Kamfanin Gruenenthal na kasar Jamus, wanda ya sarrafa maganin Thalidomide, ya nemi gafara daga dubunnnin jama'a game da haddasa nakasar jariran da ya yi.

Kamfanin ya sarrafa maganin na Thalidomide a cikin shekara ta 1950 da kuma da 60 domin amfani ga mata masu juna biyun da ke fama da laulayin ciki, wanda sakamakon hakan ya sa aka haifi dubannin yaran da basu da gabobi.

Kamfanin dai ya nuna nadamarsa a baya, amma kuma jagoranta Harald Stock, ya ce Gruenenthal ya gaza kaiwa ga ainihin iyaye matan da suka yi amfani da maganin da kuma 'yayan na su.

Masu fafitika da ma wadanda lamarin ya shafa sun ce neman gafarar ya yi kadan, kana bai zo a kan kari ba, suka kuma bukaci biyan cikakkiyar diyya.

Wannan neman gafara na fitowa ne daga bakin shugaban gugun kamfanin na Gruenenthal, Harald Stock yayin da y ke yaye lullubin mutum-mutumin da ke nuna alamar yaron da aka haifa babu gabobi sakamakon amfani da maganin na Thalidomide, yana mai cewa kamfanin ya yi matukar nadamar abinda maganinya haddasa, tare da neman afuwa daga wadanda abin ya shafa da ma iyayen su mata wadanda ya gaza kaiwa gare su a cikin kusan shekaru hamsin.

Kungiyar wadanda suka nakasa daga maganin na Thalidomide a kasar Jamus sun bayyana neman afuwar da kamfanin ya yi da cewa bai wadatar ba, kuma bai zo a kan kari ba.Daya daga cikin su cewa take.

''Ina da gajerun hannaye, kana ina fama da matsaloli a can cikin jiki na, amma kuma akwai mutane da dama da suka samu matsala sakamkon wannan magani, duk da faman da wasu kungiyoyi suka yi a cikin shekaru biyar din da suka gabata, lamarin ya kare ne ga neman gafara kawai, wannan bai isa ba, muna bukatar a biya mu diyya, a kuma nemi afuwa daga iyayanemu.''

Shugaban kamfanin na Gruenenthal, Mr Stock dai ya kara jaddada cewa kamfanin ya lura matuka da halin kunci da damuwar da mutanen suka shiga sakamakon abinda maganin na Thalidomide ya hadddasa, kuma yana mai matukar nadama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.