BBC navigation

Platini ya gargadi kulob-kulob a kan kashe kudi

An sabunta: 2 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 12:53 GMT

Michel Platini

Shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Turai UEFA, Michel Platini, ya ce ya bai wa kulob-kulob 27 wa'adi domin su daidata yadda suke kashe kudi na sayen 'yan wasan da suka aro.

Platini ya ce ya dauki matakin ne bayan da kulob-kulob da dama suka fara jinkiri na biyan 'yan wasan kudinsu.

A cewarsa, duk kulob din da bai yi biyayya ga matakin da ya dauka ba zai fuskanci yiwuwar korarsa daga shiga gasar kwallon kafa ta Turai.

Platini ya shaidawa manema labarai cewa:'' An gaya wa (kulob-kulob) cewa su daidaita yadda suke kashe kudinsu daga nan zuwa ranar 30 ga wata Yuni. Na bar su har zuwa 15 ga watan Yuli su zo idan suna da matsala game da hakan''.

Ya kara da cewa: " Za mu sanya ido ranar 30 ga watan Satumba, kuma hakan na da muhimmanci. Idan kulob-kulob suka gaza bin ka'idar da muka shimfida ta kashe kudadensu, za mu dauki mataki a kansu, ta yadda za su fice daga gasar kasashen Turai''.

Platini ya ce matakin zai kare kulob-kulob da suka sayar da 'yan wasa ga wasu kulob din kuma suke ta jewa domin a biya su, yana mai cewa sau da dama wadansu kulob-kulob kan kwashe shekaru suna bibiyar kudin da suka sayar da 'yan wasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.