BBC navigation

Ba zan sa baki a rikicin masu hakar ma'adinai ba - Zuma

An sabunta: 2 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:56 GMT
Ma'aikatan mahakar ma'adinai ta Afirka ta Kudu na zanga-zanga

Ma'aikatan Mahakar Ma'adinai ta Afirka ta Kudu masu zanga-zanga

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya ce ba zai yi katsalandan kan masu zanga-zanga kimanin dari biyu da saba'in din dake mahakar ma'adinai ta Marikana, da ake tuhuma da laifin kisan abokan aikinsu ba.

Lauyoyin wadanda ake zargi sun nemi da a saki mutanen ranar Lahadi, amma Mr Zuma ya ce ba zai bayar da kai game da bukatun ba, kana zai mutunta hukumar da ke bincikar mutuwar ma'aikatan hakar ma'adinai talatin da hudun da 'yan sanda suka bindige yayin gudanar da wata zanga-zanga a cikin watan da ya gabata.

Tuhumar da ake yiwa mahakan ma'adinan dai ta danganci ikirarin cewa sun yi wa 'yan sanda shiga hanci da kudundune, lamarin da ya haifar da matukar rashin jin dadi a kasar Afirka ta kudun.

A ranar Lahadin ne ake sa ran za a yi jana'izar wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma ministocin kasar za su ci gaba da halartar jana'izar da ake yi a sassa daban-daban na kasar ta Afirka ta Kudu, da ma makwabciyarta Lesotho.

Suna ta mika ta'aziyyar shugaba Jacob Zuma ga iyalan ma'aikatan mahakar ma'adinan, kana suna tallafawa wajen shirya yadda za a gudanar da jana'izarsu tun lokacin da wannan abin bakin ciki ya faru.

An dai dora alhakin barkewar rikicin kan gabar dake tsakanin kungiyoyin ma'aikata biyu da ba sa ga maciji da juna, wanda da farkon fari yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma, da suka hada da jami'an 'yansanda biyu.

A Makonni biyun da suka gabata ne kuma 'yan sanda suka bindige mahakan ma'adinai 34, tare da yin ikirarin cewa sun yi hakan ne domin kare kan su, wanda ya haifar da nuna damuwa a fadin kasar.

A ranar Alhamis ne kuma aka tsare tare da tuhumar wasu ma'aikatan hakar ma'adinai 270 da ake zargi da kisan abokan aikin nasu.

Ministan Shari'a na kasar Afirka ta Kudun Jef Hadebe ya nemi cikakkun bayanai daga masu shigar da kara game da daukar wannan mataki, ya ce matakin ya haifar da matukar kaduwa, tsoro da damuwa a kasar.

Yanzu haka dai lauyoyin wadanda ake tuhumar sun baiwa shugaba Zuma wa'adi daga safiyar Lahadi zuwa yamma da a saki mutanen, ko kuma su fuskanci matsin lamba daga kotu domin aikata hakan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.