BBC navigation

'Yan adawa a Zamfara sun baiwa gwamnati wa'adi

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:47 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Jam'iyyun adawa a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun baiwa gwamnatin Jihar mako biyu ta janye aniyar da ake zargin tana da ita ta korar ma'aikata dubu goma daga aiki da ta ke shirin yi.

Kakakin jam’iyyun adawan, Ahmad Sulaiman Leda, ya ce:

“Wannan abu mummunar kuntatawa ce ga ma’aikatan Jihar Zamfara…. Za mu baiwa gwamnatin wa’adi na sati biyu, kuma za mu rubutawa mai girma gwamna da jami’an tsaro cewa gwamna ya janye wannan magana”.

Sai dai Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Muhammad Birnin-Magaji, ya shaida wa wakilin BBC Abdou Halilou cewa gwamnatin ba ta ce za ta kori ma’aikata ba.

“Abin da muke cewa shi ne duk wand aba bias ka’ida [aka dauke shi aiki] ba, ko shekara dari ya yi yana [aiki, to za ya kuka da kansa]. Shi dan adawa b aka raba shi da irin wadannan korafe-korafe…”.

Wannan al’amari dai na zuwa ne a daidai lokacin da dimbin matasa a jihar da ma kasa baki daya ke ci gaba da zaman kashe wando.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.