BBC navigation

Masar ta soki Birtaniya da gaza rike dukiyar Mubarak

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:11 GMT
Gidan Gamal Mubarak a London

Gidan Gamal Mubarak a London

Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewar Birtaniya ta kyale wasu kusoshin gwamnatin tsohon shugaban kasara Masar, Hosni Mubarak su ci gaba da taba kadarorin da suka mallaka a London, duk kuwa da takunkumin da aka saka ma su.

Wasu bayanai da aka karanta, cikin wasu shafukan intanet, na nuna cewa ba a kwace wasu gine gine mallakin iyalan Hosni Mubarak , ko kuma na mukarrabansa ba. Wasu manyan jami'an gwamnatin Masar sun shaidawa BBC cewa gwamnatin Birtaniya na boye kudaden sata, tana kuma karya wasu dokoki na duniya.


Rahotannin sun nuna cewa, shugaba Hosni Mubarak da mukarrabansa sun barnatar da biliyoyin daloli, kuma hakan ya taimaka wajen rura wutar juyin juya halin da aka yi a Masar a shekarar da ta gabata.

Nan take bayan an hambarar da shi daga karagar mulki, Birtaniya ta yi alkawarin taimakawa wajen bankado dukiyoyin da aka sace, sai dai kuma sai da aka shafe wasu karin kwanaki 37 kafin a kwace wasu kadarorin Mubarak din da kuma na wasu shahararrun 'yan kasar Masar 18, wadanda kimar su ta kai kusan fan miliyan 85.

Bayanan da aka watsa a kafar sadarwa ta internet sun nuna cewa, daya daga cikin mutanen dake jerin wadanda ake tuhumar, Naglae el- Gazaely wadda mai dakin tsohon ministan gidaje ce a Masar ta yi rijista da wani kamfani a London da sunanta tun a watan Nuwambar bara, watanni bakwai bayan bada umarnin a kwace kadarorin nata.

Yanzu haka dai Masar ta kai Birtaniya kara kotu, domin samun cikakken bayani akan kadarorin da aka kwace.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.