BBC navigation

Yawan man da Najeriya ke fitarwa ya ragu

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:19 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Wani rahoton da Babban Bankin Najeriya ya wallafa shafinsa na intanet ya ce gangar danye mai miliyan biyu da dubu dari da ashirin kasar ta fitar zuwa kasashen waje a kowace rana daga watan Afrilu zuwa watan Yuni na bana.

A cewar Babban Bankin na Najeriya, daga watan Janairu zuwa Maris, gangar mai miliyan biyu da dubu dari shida kasar ta fitar zuwa kasashen waje a kowace rana, abin da ke nuni da cewa an samu karuwa a yawan fetur din da kasar ke fitarwa a kowace rana.

Sai dai duk da haka, adadin adadin bai kai abin da ma’aikatar kudi ta saka a cikin kasafin kudi na bana ba, a matsayin abin da ake sa ran samu.

Wadansu dai na ganin wannan al’amari na iya jawo koma-baya ga tattalin arzikin kasar.

'In aka ci gaba da haka za a samu matsala'

Wani masanin harkar hako mai a kasar ta Najeriya, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ya ce idan hakan ya ci gaba, to za a samu matsala wajen aiwatar da kasafin kudin.

“Akwai asusun ajiyar rarar man fetur—idan aka samu raguwa a kana bin da aka yi hasashen samu kamar yadda aka samu yanzu, ana iya diba daga asusun a ci gaba da gudanar da abubuwa…”.

Sai dai kuma kakakin Kamfanin Mai na Kasar, wato NNPC, ya ce Babban Bankin ya yi amfani ne da tsohon bayani, amma kuma bai yi wani Karin bayani ba.

Babban Bankin dai ya ce sashensa na bincike ne ke nazari bayan duk wata uku a kan yawan man fetur din da kasar ke fitarwa ko hakowa a kowace rana kuma yana amfani da hanyoyi da dama wurin tatttara bayanansa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.