BBC navigation

Kwamitin gasar Paralympics ya yi watsi da koken Pistorius

An sabunta: 3 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:10 GMT
'Yan gasar wasan tsere na Paralympics

'Yan gasar wasan tseren mita 200 na Paralympics

Kwamitin gasar wasan nakasassu ta duniya Paralympics, ya yi watsi da koken da dan wasan tsere na kasar Afirka ta Kudu, Oscar Pistorius ya gabatar cewar ba a yi adalci a wasan ba.

Yayin da yake magana bayan ya zo na biyu kan takwaransa na kasar Brazil Alan Olivera, Pistorius ya yi suka game da tsayin kafar tseren abokin karawar ta sa, yana mai cewa tsawonsu na da ban mamaki.

Kwamitin na IPC dai ya ce an riga an gwada tsayin kafafuwan, ya ce kuma babu batun keta hakkin dokar wasannin.

Dan wasan tseren kasar Brazil, Alan Olivera ya samu nasarar cin lambar zinari a tseren mita 200 na gasar wasan nakasasu ta duniya Paralympics da ake gudanarwa a birnin London wanda aka watsa yadda ya ke gudana kai tsaye a gidan rediyon BBC na Radio 5.

Olivera ya samu galaba ne kan abokin karawar ta sa mai tagomashi, Oscar Pistorius na kasar Afirka ta Kudu, wanda kuma ya kalubalanci nasarar da Alan din ya samu da cewa an yi kwange a wajen auna tsawon kafafuwan gudu na karfe da aka yiwa dan wasan.

Mr Pistorus yayi kakkausar suka da yadda gasar wasan ta kasance, yana mai cewar masu shirya gasar ta Paralympics na bukatar su duba lamarin da kuma abubuwan da dokar gasar wasannin ta tanada.

Abokin karawar ta sa, wanda ya samu galabar wato Alan Olivera ya ce Mr Pistorius ya yi mummunar fahimta ne, yana mai cewa sai da alkalan wasa suka duba tare da tantance kafafuwan karfen nasa.

Hukumar shirya gasar wasan nakasassun ta Paralympics IPC dai ta ce ba ta yi wani abu da ya kaucewa dokar da gasar wasannin duniyar ta tanada ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.