BBC navigation

'Yan gudun hijirar Syria sun haura 100,000 a Agusta

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:30 GMT
'Yan gudun hijirar Syria

'Yan gudun hijirar Syria sun haura 100,000 a watan Agusta

Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ’yan kasar Syria sama da dubu dari ne suka tsere daga kasar a cikin watan Agusta, adadin da shi ne mafi girma da alkaluman da ake tattara kowanne wata suka nuna tun daga lokacin da aka fara rikici a watan Maris na bara.

Hukumar ta ce rikicin ya kazanta.

’Yan gudun hijirar da ke kasar Labanon suna zaune ne a makarantun da yanzu ake gaf da bude su don fara karatu—dole ne ke nan su bar wajen.

Yayin da aikin agaji yake ci gaba da fuskantar koma baya a kasar, shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross, Peter Maurer, ya gana da shugaban Syria Bashar al-Assad a birnin Damascus.

Mista Maurer ya bukaci Shugaba Assad ya baiwa masu aikin agaji damar shiga yankunan kasar don taimakawa wadanda rikicin ya rutsa da su.

Mutanen kasar da suka yi gudun hijira zuwa Turkiyya sun bayyana halin da suka tsinci kansu kafin su bar kasar.

Daya daga cikinsu ya ce “dakarun sojin Syria dubu goma sha uku ne suka zagaye garinmu; kimanin mutane dubu hamsin ne suke zaune a birnin, amma yanzu mutane dubu ashirin da biyar sun bar garin—garin namu ya fuskanci tsananin barin wuta na tsawon kwanaki biyu”.

Mutane dubu daya ne suke yin gudun hijira zuwa kasar Jordan a kowacce rana, wadansu dubu tamanin kuma sun isa Turkiyya.

Hakazalika dubu tamanin na jira a bakin iyakar kasar ta Syria, yayin da hukumomin agaji ke kokarin bude musu sansanin 'yan gudun hijra.

A bangare daya kuma kasar Iraqi na ganin cewa dubban mutanen kasar da suka yi gudun hijira a lokacin nata rikicin zuwa Syria suna dawowa Iraqi duk da cewa ba su da muhalli; amma sun yi amanna cewa za su fi samun kwanciyar hankali a kasar fiye da Syria.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.