BBC navigation

Takaddama kan karin mazabu a kasar Ghana

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:19 GMT
Kasar Ghana

Kasar Ghana

A kasar Ghana, wata takaddama ta kunno kai game da yunkurin hukumar zaben kasar na kara yawan kujerun majalisar dokokin kasar daga 230 zuwa 275.

Ita dai jam'iyyar adawa ta NPP ta nuna adawarta da kirkiro da sabbin mazabun wanda zai bada damar samar da sabbin kujeru a majalisar dokokin kasar yayin da ya rage watanni hudu a gudanar da babban zaben kasar.

Karin yawan kujeru 45 a majalisar kasar da hukumar zabe ke da kudirin yi, ya janyo cacar baki.

Bangaren marasa rinjaye tare da kungiyoyin fararen hula, sun yi korafin cewa hukumar zaben kasar ta kasance 'yar amshin shatar jam'iyar NDC mai mulkin kasar, tare da zargin cewa jam'iyar ta NDC na son ta mamaye zauren majalisar gabaki daya.

Jam'iyar ta NDC ta mayar da martani tare da musanta zargin cewa tana yunkurin yin magudi tare da yin babakere a zauren majalisar kasar.

Ita ma hukumar zaben kasar ta ce ba gudu ba ja da baya a kirkiro da sababbin mazabun.

Mataimakin shugaban hukumar zaben kasar Alhaji Sulley Amadu ya ce ba wannan ne karon farko da za su kara yawan mazabu a kasar ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.