BBC navigation

Najeriya za ta bunkasa noman kwakwar man ja

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT
Kwakwar man ja

Kwakwar man ja a Indonesia

Ma'aikatar noma ta Najeriya ta bayar da alwashin cewa, idan har aka bunkasa harkar noman kwakwar man ja, to za ta rika sama wa kasar kudaden shiga akalla Dalar Amurka biliyan takwas kwatankwacin fiye da naira trillion daya a ko wacce shekara.

A shekarun baya dai kwakwar man ja na daya daga cikin muhimman kayan amfanin gona a yankin kudancin kasar da ke samar da makudan kudade ba wai ga manoma kadai ba, har ma da habbaka tattalin arzikin kasar.

A sakamakon haka ne gwamnatin kasar ta ce za ta farfado da wannan fanni na noma, ta hanyar tabbatar da ganin cewa an yi sabbin shuka na kwakwar man ja kimanin kadada dubu dari biyu da hamsin a jihohi goma sha daya na kudu maso yamma, kudu maso gabashi, da kuma kudu maso kudu na kasar a cikin shekaru biyu zuwa uku masu zuwa.

Kayan aiki dai kan zamewa manoman Najeriya musamman kanana wata babbar matsala, ko da yake gwamantin kasar ta ce za ta yi amfani da wasu kamfanoni masu zaman kan su na cikin gida da na kasashen waje da za su taimaka dan kawo injinan sarrafa man jan.

Manoman kwakwar man jan da dama na cewa suna nan suna dakon wannan shirye-shirye da aka yi, saboda sun yi amannar za su iya samar da fiye da adadin man jan da suke sa ran za su iya samarwa idan aka tallafa musu yadda ya dace.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.