BBC navigation

Al-Senussi ya shiga hannun hukumomin Libya

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:30 GMT
Abdallah Al-Senussi

Abdallah Al-Senussi

Hukumomin Libya sun tabbatar da cewa tsohon shugaban hukumar leken asiri a zamanin mulkin Gaddafi wato, Abdallah Al-Senussi ya shiga hannunsu bayan tuso keyarsa daga Mauritania.

Libya dai na son ta gurfanar da Mista Senussi a kan zarge-zargen aikata manyan laifuka a lokacin gwamnatin marigayi Gaddafi.

Haka kuma ana neman Senussi a Faransa da kuma Kotun hukunta manyan laifukan yaki na duniya wato ICC.

Da fari dai Mauritaniya ta ce sai Senussi ya fuskanci tuhuma game da shiga kasar da ya yi ba da izini ba.

Tsohon shugaban hukumar leken asirin kuma na hannun damar Gaddafi ya tsere daga Libya ne a bara, bayan an kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi.

Kuma da shigarsa Mauritaniya aka cafke shi, inda sabuwar gwamnatin Libya ta yi ta kiraye-kirayen a tasa keyarsa gida.

Labarin mika shi ga Libyan dai an watsa shi ne ta gidan talabijin din Mauritania.

Kuma kawo yanzu babu wani tabbaci game da hakan daga hukumomin Libyan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.