BBC navigation

Mali ta nemi akai dakarun Afrika kasar

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:02 GMT

Kasar Mali

Jami'an diplomasiyya na Faransa sun ce gwamnatin Mali ta nemi Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma ta tura dakarun ta kasar don kawo karshen rikicin siyasar da ake yi sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar cikin watan Mayu.

Wani babban jami'in Faransa ya ce Shugaban rikon kwarya na kasar ta Mali Diancounda Traore ne ya nemi kungiyar ta ECOWAS ta taimaka wajen sake kwato arewacin kasar dake karkashin ikon 'yan kishin Islama.

Dama dai ECOWAS ta yi tayin tura dakarun na ta fiye da dubu uku zuwa kasar Malin don daidaita al'amurra a kasar.

Sai dai masu nazarin alamurra na ganin daukar matakin soji ba lalle ne ya kawo karshen rikita rikitar da ake fama da ita a kasar ta Mali ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.