BBC navigation

Sabon rahoto kan ta'adin ambaliyar ruwa a Nijar

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 21:23 GMT
Ambaliyar ruwa a Nijar

Ambaliyar ruwa a Nijar

A jamhuriyar Niger hukumomin kasar sun fitar da wani sabon rahoto a kan irin ta'adin da matsalar ambaliyar ruwa ta haddasa a kasar.

Rahoton dai ya ce akalla mutane 62 ne suka rasa rayikansu, kuma wasu karin dubu dari biyar sun rasa muhallansu a sakamakon ambaliyar ruwan.

Har illa yau rahoton ya kunshi bayanai game da taimakon da ya zuwa yanzu gwamnatin ta samu daga ciki da wajen kasar domin taimaka wa wadanda ambaliyar ta rutsa da su.

Daga cikin tan dubu shida da dari biyu da talatin da biyu na abinci da ake bukata domin tallafawa wadanda matsalar ta raba da gidajensu, gwamnatin ta tabbatar cewa ta yi nasarar tattara tan dubu hudu da dari biya.

Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar ta Nijar sun yi kira ga gwamnatin da ta sake duba tsarin raba taimakon ta yadda zai kai ga duka wadanda lamarin ya ritsa da su a duka sassan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.