BBC navigation

'Yan fashin teku a Najeriya sun yi fashin Jirgin Singapore

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 10:12 GMT
Wani jirgin Koriya ta Kudu da 'yan fashi suka kwace

Matsalar fashin teku na cigaba da zama babbar kalubale ga kasshen duniya

'Yan fashin teku sun yi fashin wani jirgin ruwa mai dakon mai, mallakar kasar Singapore a gabar tekun Najeriya.

Kakakin sojin ruwan Najeriya ya tabbatar wa BBC da aukuwar al'amarin.

Jerry Omodara ya ce kawo yanzu babu cikakken bayani game da inda jirgin yake, amma ana kokarin gano shi.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Faransa, AFP cewa ma'aikatan jirgin 23 na cikin jirgin a lokacin da aka yi fashinsa, kuma sun kulle kansu a wani daki.

Masu sharhi sun ce ana samun karuwar fashin jiragen ruwa a wasu sassan yammacin Afrika.

A watanni shida da suka gabata, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa ta ce an samu fashin jirage 17 a ruwan Najeriya a shekarar 2012 kadai, wanda jimillar ta haura na bara.

Hukumar ta shaidawa AFP cewa jirgin dakon man an yi fashinsa ne a ranar Talata, a tashar jiragen ruwa dake Legas.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.