BBC navigation

Sojin Najeriya sun ceto jirgin Singapore

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:54 GMT

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce ta kwato jirgin ruwa mai dakon mai, mallakar Singapore da wasu 'yan fashin teku suka yi fashi a gabar tekun kasar.

Kakakin rundunar ya ce ma'aikatan jirgin su 23 suna cikin koshin lafiya, kuma ana raka jirgin ruwan zuwa tashar jiragen ruwa na Legas.

Jerry Omodara ya kara da cewa 'yan fashin sun tsere daga jirgin mai suna Abu Dhabi Star.

Rundunar sojin ruwan ta tura jirage yaki biyu da kuma jirgi mai saukar ungulu domin ceto jirgin ruwan da aka yi fashin.

'Yan fashin teku sun yi fashin jirgin ruwa na Singapore ne a ranar Talatar da ta gabata.

A watanni shida da suka gabata, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa ta ce an samu fashin jirage 17 a ruwan Najeriya a shekarar 2012 kadai, wanda jimillar ta haura na bara.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.