BBC navigation

Danbindiga ya harbe mutane a Quebec na Canada

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:48 GMT
Pirimiyar Pauline Marois

Pirimiyar Pauline Marois

Wani dan bindiga a Canada ya bude wuta a lokacin da sabuwar zababbiyar Pirimiyar Lardin Quebec take gudanar da wani jawabi bayan samun nasarar da ta yi a zaben lardin, inda ya hallaka mutum guda, ya kuma jikkata wasu.

Ma'aikatan tsaro dai sun kakkare Primiyar Pauline Marois ta jam'iyyar 'yan awaren ta Quebecois.

Tana bayyana bukatar ta ta ganin cewar lardin wanda masu magana da harshen Faransanci suka fi rinjaye, ya balle daga Canada keda wuya wani mutum mai shekaru 62 da haihuwa, ya kutsa cikin otal din kuma ya harbe mutane biyu, inda daya daga cikinsu ya mutu nan take sannan dayan kuma yana asibiti, rai kwakwai, mutu kwakwai.

Tuni dai 'yan sanda suka damke mutumin.

Har ila yau, nan take ne kuma jami'an tsaron suka dauke Pauline Marois daga dandalin da take jawabi don a kubutar da ita.

Ita ma shugabar jamiyyar adawa ta Green Party a Canada, Elizabeth May ta ce bayyana takaicinta game da lamarin.

Wannan lamarin dai ya kawo cikas a bukin murnar samun nasarar Jami'yyar Quebecois wacce ke kokarin kafa gwamnatin marasa rinjaye a Quebec.

Jam'iyyar dai nada aniyar ficewa daga cikin sauran kasar Canada.

ita dai Pauline Marois ta bayyana muradin ganin cewar Quebec ta zama kasa mai cin gashin kanta.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.