BBC navigation

Brahimi ya kadu da rikicin Syria

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:55 GMT
sabon wakilin majalisar dinkin duinya a Syria

Brahimi

Sabon wakilin Majalisar Dinkin Duniya ga kasar Syria Lakhdar Brahimi ya bayyana adadin mutanen dake mutuwa a kasar a matsayin wani abin kaduwa yayinda ya kira ragargaza kasar da ake yi a matsayin wani bala'i.

A jawabinsa na farko ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya tun bayan nada shi a ranar assabar Mr Brahimin ya ce zai ziyarci kasar ta Syria cikin wasu 'yan kwanaki masu zuwa.

Sabon waikilin ya yi kuma kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta ba shi goyan baya wajen sauke nauyin dake kansa.

Yace, goyon bayan al'ummar kasashen duniya wani abu ne mai muhimmanci.

Tun farko babban Sakataren Majalisa Dinkin Duniya Ban ki moon ya zargi kasashen dake aika wa gwamnatin Syria makamai da laifin yada bakin ciki da bacin rai.

Mr Ban din dai bai ambaci kasa ko guda ba, to amma Rasha, ita ce babbar kasar dake sayar wa gwamnatin Shugaba Assad makamai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.