BBC navigation

Malema ya bukaci masu hako maadanai su ci gaba da yajin aiki

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:08 GMT

Julius Malema


Dan fafutukar nan mai tsattsauran ra'ayi na Afrika ta Kudu Julius Malema ya sabunta kiran da ya yi ga ma'aikatan dake yajin aiki su mayar da wuraren hakar ma'adinan kasar a matsayin wuraren da za a ji wahalar tafiyar da su.

Ya gaya wa BBC cewa ba ya goyon bayan tashin hankali, to amma ya ce kamata ya yi ma'aikata a mahakar ma'adinan su jingine aiki, har sai an yi musu karin albashi.

Yace, mutane suna ta magana a kan wannan batu na wahalar tafiyar da lamuran hako ma'adanan.

Acewar sa yana nufin su cigaba da yajin aiki, ba wai yana kiran a tayar da husuma ba ne."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.