BBC navigation

Bill Clinton ya yi nuni a zabi Obama

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:31 GMT

Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton ya bayyana dalilan da suka sanya yake ganin yakamata a sake zaben Shugaba Obama a taron jam'iyyar da ake yi a North Carolina.

Bill Clinton

Mr Clinton yace ya goyi bayan tsaida Barack Obama ne a wani wa'adin mulkin karo na biyu saboda mutum ne mai tsananin kishin kasa a zuciyar sa, amma a waje za a ga kamar yana da sanyin jiki.

Mr Clinton din yace Mr Obama ya kare tattalin arzikin Amurka daga durkushewa a farkon wa'adin mulkin sa, zai kuma kirkiro gurabun ayyukan yi nan gaba.

Tsohon shugaban kasar na Amurka, Bill Clinton ya yi ta zayyano dalilan sa na ganin Obama ya cancanci ya zama shugaban kasar Amurka da kuma yadda akidun Jamiyyar Democrat suka sha bamban acewar sa da na Republican.

Bill Clinton ya ce yana so ya zabi mutumin da ya hau karagar mulki don ya gyara tattalin arzikin da tuni yayi rauni kuma ya hana tattalin arzikin durkushewa baki daya ya sa kasar tafarkin farfadowa na dogon zango.

Toshon shugaban ya ce yanason zabar wanda yayi imanin cewa zai gina sabuwar Amurka mai tattalin arzikin da kirkire kirkire da ilimi da kuma hadin kai ya haifar da shi.

Ya kara da cewa yana son Barack Obama ya sake zama shugaban kasar Amurka yana kuma tunkaho da nunashi a matsayin dan takarar Jamiyyar Democrat.

A jawabin da ya yi mai tsawo don nuna fifikon Jamiyyar Democrat kan Republican, tsohon shugaban Bill Clinton ya ce abun tambayo mai mahimmanci shine, wace irin kasa kake son zama a cikin ta? Shin kana son kasa mai mulkin wadda ba ruwanta da kai, kayi ta kanka, to sai ka zabi Republican. Amma idan kanason kasa mai gwamnatin da take tafiya da kowa da kowa kuma kowa nata ne, to ai sai ka zabi Barack Obama.

Tun farko dai uwar gidan shugaban kasar Amurka Michelle Barack Obama ta nuna irin jan aikin da Barack Obaman yayi da kuma yanayin rayuwar sa wadda acewar ta take nuni da cancantar sa ya sake zama shugaban kasar Amurka.

A daren yau ne dai shugaba Barack Obama zai yi jawabin karbar tikitin Jamiyyar na zama dan takarar Jamiyyar a zaben kasar mai zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.