BBC navigation

Dalilan mayarwa Dana Air na Najeriya lasisi

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:40 GMT
Ranar 3 ga watan Yuni wani jirgin Dana Air ya yi hadari

Ranar 3 ga watan Yuni wani jirgin Dana Air ya yi hadari

Ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya, Stela Odua, ta sanar da hujjojin da suka sa ma'aikatarta ta mayarwa kamfanin Dana Air lasisinsa don ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.

Hakan kuwa na wakana ne bayan kwanaki casa’in da biyar da aukuwar hadarin wani jirgin sama na kamfanin na Dana Airline a Lagos da ke kudancin kasar, hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari da hamsin.

Yayin wani taron manema labarai ne dai ministar, Uwargida Stela Odua, ta bayyana cewa:

“Akwai sakamakon binkicen farko, akwai sakamakon bincike na karshe, kuma hukumar kula da kariyar sararin samaniya na ci gaba da gudanar da bincike.

“Hakan kuma na cikin ka’idojin ayyukan jiragen sama—jirgin kamfanin jiragen sama na kasar Kenya ya yi hadari, jirgin kamfanin Air France ya yi hadari, haka ma jirgin kamfanin British Airline ya yi hadari, an samu asarar rayuka, amma kuma suna ci gaba da ayyuka ba a rufe kamfanonin ba”.

Ta kuma kara da cewa, “A sha'anin zirga-zirgar jirage, kariya na da muhimmanci; za a ci gaba da gyare-gyare da bunkasa al’amura.

“A gaskiya mun ma yi abin da ba a taba yi ba da muka dakatar da su”.

A halin yanzu dai kamfanin na Dana Airline zai ci gaba da daukar fasinjoji kamar yadda aka saba.

Sai dai fatan jama'a shi ne a ci gaba da bunkasa al’amuran zirga-zirgar jiragen sama kamar yadda suke a cikin kasashen duniya da su ka ci gaba, domin rage yawan hadura da ke lakume dubban rayukan jama'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.