BBC navigation

An hallaka mutane 12 a sabon rikicin Kenya

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:49 GMT
Taswirar Kenya mai  nuna yankin Kogin Tana

Taswirar Kenya mai nuna yankin Kogin Tana

An hallaka mutane goma sha biyu a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin gabar tekun Kenya.

Wani wanda ya shaida faruwar al'amarin ya shaidawa BBC cewa da safiyar ranar Juma'a ne mahara dauke da muggan makamai suka banka wuta a kauyen Cham-wana-muma da ke gabar tekun Tana, sannan suka tattara dabbobi suka yi gaba da su.

Wani mazaunin gabar tekun na Tana, Timson Maneno, ya ce mutanen kauyen na shirin binne wadanda suka rasu sakamakon harin.

“Wadansu mutane ne dauke da muggan makamai suka shigo kauyen—suna sanye ne da kakin soji.

“Sun mamaye kauyen Cham-wana-muma, inda suka kashe mutane goma sha biyu, wadanda suka hada da maza biyar, da mata shida, da kuma wani yaro; hankulan mutane sun yi matukar tashi, kuma a halin da ake ciki ana shirin binne mutanen da suka mutu”.

An yi ta yin taho-mu-gama tsakanin kabilar Pokomo, wadanda manoma ne, da kuma kabiliar Orma, wadanda makiyaya ne, sanadiyar filayen kiwo da wuraren ban ruwan dabbobi.

An kashe fiye da 50 makwanni biyu da suka wuce

Makwanni biyun da suka gabata ma dai fiye da mutane hamsin aka kashe a yankin.

An bayyana harin na baya-bayan nan da cewa ramuwar gayya ce ta ’yan uwan mutanen da aka kashe a baya.

Sai dai hukumomi a kasar na ganin harkokin siyasa na taka rawa a hatsaniyar da ake yi tsakanin kabilun, ganin cewa ana dab da gudanar da babban zaben kasar a farkon shekara mai zuwa.

A gefe guda kuma, masu sharhi na ganin cewa yanayin rabon iko a kasar—inda yawanci aka fi samun mukaman gwamnati a yankunan karkara—ne ke haddasa irin wadannan matsaloli a wadansu yankuna na kasar.

Shekaru biyun da suka gabata ne dai kasar ta Kenya ta samar da sabon kundin tsarin mulki, wanda a karo na farko ya samar da mukaman gwamnoni da kuma majalisun jihohi.

A lokacin da aka kai hari na farko a watan jiya, gwamnati ta yi alkawarin magance matsalar, sannan ta hukunta mutanen da aka samu da laifi.

Sai dai harin da aka kai a baya-bayan nan ya sanya mutane na ganin cewa gwamnati ba za ta iya samar da cikakken tsaro a kasar ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.