BBC navigation

Obama ya yi kira a zabi Demokrat

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:04 GMT

Barack Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi jawabi a babban taron Jamiyyar Democrat a North Carolina inda ya amince ya zama dan takarar Jamiyyar na shugaban kasa karo na biyu.

Mr Obama yace muradan da yake son cimmawa sune batun kirkirar aiyukan yi, rage bashi da kuma sanya tattalin arzikin kasar ya kara karfi.

Ya bayyana zaben a matsayin wani zabi kan tafarki mabambanta guda biyu ga makomar Amurka.

Obama Dan takarar Democrat

Jawabin da shugaban kasar Amurka Barack Obama yayi na da tsawo da shiga jiki, inda shugaban ya ce ya amince da ya sake zama dan takarar shugaba kasa na Jamiyyar karo na biyu

Shugaban ya nuna abubuwan da zai ci gaba da tunkara gadan-gadan wadanda a acewar sa zai kara bunkasa tatalin arzikin kasar gami da samar da aiyukan yi.

Shugaban kasar wanda ya bayyana matarsa Michelle a matsayin masoyiyarsa yace shekaru kadan masu zuwa za a dau matakai masu inganci a Washington kan samarda aiyukan yi da tattalin arziki da makamashi da ilimi, matakan da inji Obaman zasu yi amfani matuka ga rayuwar Amurkawan.

Ya ce zaben dai wani maauni ne na tafarki guda biyu mabamabanta amma na su tafarkin shine tabbatar da hanyoyin da za su gina matsakaitan rukunin alumma da kananana masana'antu da kuma karfin tattalin arziki wanda ba a taba sanin sa ba a duniya.

Da dukkan alamu dai zaa fafata tsakanin Barack Obama na Jamiyyar Dmocrat da Kuma Mitt Romney na Republican inda kuriuin raayoyin jamaa ke nuni da cewa suna kusa da kusa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.