BBC navigation

JTF ta tabbatar da kashe 'yan bindiga a Maiduguri

An sabunta: 8 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:29 GMT
jami'an tsaro na bincike a Nijeiya

jami'an tsaro na bincike a Nijeiya

Sojin Najeriya sun ce sun kashe wasu da suke zargin 'yan kungiyar gwagwarmayar Islaman nan ce ta Boko Haram, a wani artabu da bindigogi a arewacin kasar.

Wani kakakin soji ya ce an kama wasu mutanen sha uku(13), bayan wani hari a kan wani wurin duba ababen hawa na soji a birnin Maiduguri.

Tashin hankalin ya faru ne kwana daya bayan da 'yan sandan Najeriyar suka ce za su rinka sintirin ba- dare-ba-rana, a kan wuraren da aka girke na'urorin sadarwa na wayoyin salula.

Hakan ya biyo bayan hare hare a kan irin wadannan na'urori ne da dama da aka kai a arewacin Nijeriyar.

A wani lamarin na daban 'yan sanda a birnin Bauchi sun harbe wani ma'aikacin gwamnati har lahira.

Ma'aikacin da ne ga Alhaji Umaru Dahiru, wani tsohon kusa a jam'iyyar PDP.

'Yan sanda sun ce sun bude wa motarsa wuta ne, bayan da suka tsayar da shi ya ki tsayawa.

An kuma ba da rahotannin tashin bama-bamai a wata anguwa ta garin na Bauchi, amma babu labarin wani da ya jikkata.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.