BBC navigation

An yanke wa Hashemi hukuncin kisa a Iraki

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:19 GMT
Tariq al-Hashemi, mataimakin shugaban Iraki

Tariq al-Hashemi, mataimakin shugaban Iraki

Wata kotun Iraqi ta yanke wa mataimakin shugaban kasar da ake nema ruwa-a-jallo, Tariq Al Hashemi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
An same shi ne da laifi kan gudanar da wasu rundunoni dake kashe 'yan Shi'a da kuma jami'an tsaron kasar.

Tariq Al Hashemi, wanda mabiyin mazhabar Sunni ne, ya tsere daga kasar ta Iraqi a farkon shekarar nan kuma yanzu haka yana zaman gudun hijira a Turkiyya.

Wannan batu dai ya haifar da rudani dangane da tsarin rabon iko a gwamnatin Iraqin tsakanin 'yan Sunni, da 'yan Shi'a, da kuma Kurdawa.

Tariq al-Hashemi, wanda ya musanta zargin bai halarci zaman kotun da aka yanke masa ba a bayan idanunsa. Ya tsere daga kasar ne bayan da aka zarge shi da ayyukan ta'addanci cikin watan Disamba.

Tsit kake ji a cikin zauren kotun a birnin Bagadaza, lokacin da alkalin, wanda ya ce ba za a bayyana sunansa ba, saboda tsoron kai masa harin ramuwar gayya, ya bayyana hukuncin, inda ya yanke wa Al-Hashemi da surukinsa hukuncin na kisa, bisa zargin kashe wani lauya, da kuma wani jami'in tsaro.

Wani mai magana da yawun al-Hashemi ya ce ba zai yi sauran furta komai ba, kuma mataimakin shugaban kasar zai fitar da sanarwa nan gaba a yau.

Cikin watannin baya aka fara shari'ar, kuma kotun ta yi zama kamar sau goma kan batun.

Daga cikin shaidun da suka bayyana a gaban kotun har da wani tsohon mai tsaron lafiyar mataimakin shugaban kasar, wanda ya ce an biya su kudi, aka kuma umurce su su kai hare haren.

Shi dai al-Hashemi na ikrarin cewa akwai alamun an azabtar da masu tsaron lafiyar nasa ne, ko kuma an matsa masu lamba, har suka fito suka bada shaida a kansa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.