BBC navigation

Pistorius ya yi nasara a gasar nakasassu

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:20 GMT

Oscar Pistorius

Dan tseren nan na Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius, ya yi nasarar kare kambunsa a tseren mita 400 a gasar nakasassu da ake dab da kammalawa a birnin London.

Dubban jama'a ne dai suka yi ta yi masa sowa a lokacin da ya yi nasarar samun lambar zinare a karon farko a birnin London a rana ta karshe a gasar.

Shi dai dan wasan ya yi wa sauran abokan karawarsa fintinkau ne inda ya yi nasarar kafa sabon tarihi a gasar ta Paralympics.

A makon jiya ne dai Mista Pistorius ya yi ta tayar da jijiyar wuya bayan da ya zo na biyu a tseren mita 200, inda ya nemi da a gudanar da bincike a kan tsawon kafar karfe ta abokin karawarsa, Allen Olivera, wanda ya lashe gasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.