BBC navigation

Ana gudanar da zabe a Hong Kong

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:55 GMT

Wata mata a kusa da hotunan wasu 'yan takarar Majalisar Dokokin Hong Kong

A ranar Lahadi ne al'umar Hong Kong ke gudanar da zaben Majalisar Dokoki wanda ake gani zai bai wa mutanen da suka balaga da kananan yara damar jefa kuri'unsu.

Za a yi zaben ne don cike gurbin fiye da rabi na kujerun Majalisar Dokokin, yayin da su kuma masu ruwa-da-tsaki na yankin za su bayar da sunayen mutanensu don cike guraben sauran kujerun.

Ana sa-ran masu rajin kare mulkin dimokaradiyya za su taka rawa a zaben.

Ranar Juma'a gwamnatin yankin ta yi amai ta lashe a kan shirinta na bullo da darussan dole a kan kishin kasar China, bayan da dubun dubatar masu zanga-zanga suka hau kan tituna don bayyana bijirewarsu ga shirin.

Samun goyon bayan Majalisa

Tun lokacin da Hong Kong ta dawo karkashin mulkin China shekaru goma sha biyar da suka gabata, jama'arta ke fafutukar ganin kowa ya samu damar kada'a kuri'arsa.

Ana ganin jama'ar na kan hanyar cimma burinsu a zaben da za a gudanar a shekarar 2017.

Sai dai hakan zai faru ne idan aka dauki wasu matakai, ciki har da samun goyon bayan 'yan majalisun dokokin kasar da za a zaba ranar Lahadi.

Shi yasa ake sanya ido sosai a kan zaben.

A zabukan da suka gabata dai, masu rajin mulkin dimokaradiyya sun samu kashi daya cikin uku na kujerun majalisun dokokin.

Sun kara samun farin jini ne bayan da aka yi ta yin zanga-zangar kin jinin China a shekarar da muke ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.