BBC navigation

An dankawa Afghanistan fursunonin Bagram

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:59 GMT
Wani gidan yari

Wani gidan yari

Rundunar sojin Amurka a Afganistan ta mika wani gidan kurkuku da ake ta takaddama a kansa ga hukumomin Afganistan.

Fursunoni kusan 3000 na gidan yarin dake Bagram a arewacin Kabul sun koma karkashin ikon Afganistan.

Sai dai duk da nuna kin amincewa daga Afghanistan, Amurka ta cigaba da rike tare da kula da daruruwan fursunoni, ciki har da wadanda aka tsare su a baya-bayan nan da kuma wasu 'yan kasashen waje.

Mika kurkukun wani bangare ne na yunkurin mika baki daya gidajen yari ga hukumomin Afghanistan, gabannin janyewar dakarun tsaro na NATO nan da shekaru biyu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.