BBC navigation

An kashe mutane 30 a rikicin kabilanci a Kenya

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:13 GMT
Tashin hankali a Kenya

Wasu matasa dauke da makamai a Kenya

A kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a wani sabon tashin hankali dake da nasaba da kabilanci a kudu maso gabashin Kenya.

Cikin wadanda suka mutu a harin da wasu daruruwan mutane suka kai a kan wani kauye sun hada da kananan yara da kuma jami'an 'yan sanda.

Kawo yanzu kusan mutane dari ne suka mutu a tashe-tashen hankulan da ake samu a gabashin gundumar Kogin Tana tun a watan jiya.

Kabilun dake gaba da juna sun dinga kaiwa juna hari a kan shanu da burtali, a yankin da ya fi kowanne talauci a Kenya.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce a tashin hankalin na baya-bayan nan, wasu mutane kimanin 300 ne suka kai hari a kan wani kauye mai suna Kilelengwani tare da kona gidaje 167.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.