BBC navigation

Shugaban AlQaida Makhloufi ya mutu a Mali

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:13 GMT
Mayakan kungiyar Ansar Dine a kasar Mali

Mayakan kungiyar Ansar Dine a kasar Mali

Wani kwamandan 'yan fafutuka da ake dangantawa da kungiyar AlQaida a yankin Magreb ko AQIM, wanda kuma aka yiwa lakani da Sarkin Sahara, Nabil Makhloufi ya mutu a hatsarin mota a Mali.

Wani mai magana da yawun kungiyar masu fafutukar Islama ne ya bayyana hakan.

Makhlouf wani kusa ne a kungiyar AlQaida dake yakin Magreb wato AQIM, kungiyar da ake zargi da sace wa tare da kashe 'yan kasashen waje a fadin Hamadar Sahara.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, kakakin kungiyar masu fafutukar Islamar ta Ansar Dine, Abou Mohamed ya ce Makhloufi dan kasar Algeria da aka fi kira da lakabin Nabil Alqama ya mutu a hatsarin mota a kusa da birnin Gao a ranar Lahadi.

A watan Aprilun da ya gabata ne, masu fafutukar suka kwace arewacin kasar.

Kungiyar kawancen tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, ECOWAS ta ce ta shirya kai dakaru dubu uku masu karfi domin cin galabar masu fafutukar.

Hakan na zuwa ne lokacin da ake cigaba da nuna damuwar cewa, masu fafutukar za su iya wargaza baki daya yankin arewacin kasar.

Sai dai kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya bai kai ga bada amincewarsa ba, saboda fargabar rashin fitowa karara a bayyana abubuwan da dakarun za su cimma a can.

Haka kuma akwai yiwuwar dakarun su tsinci kansu cikin wani yaki da ba a san ranar kare shi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa, wani jami'in diplomasiyyar Algeria ya tabbatar da rasuwarsa.

Ayyukan AQIM

Makhloufi mataimaki ne ga Abdelhamid Abu Zeid, daya daga cikin shugabannin kwamandojin AQIM a yankin Sahara.

AQIM ta kashe 'yan kasashen waje da dama, cikinsu har da wani Bafaranshe, Michel Germaneau da kuma wani dan BIrtaniya Edwin Dyer bayan aN tsare su a Mali a shekarar 2010.

A shekarar da ta gabata an kashe wani bajamushe, kuma kungiyar ta yi garkuwa da wasu 'yan kasar waje guda uku a Tumbuktu, garin da ya shahara wajen yawon bude ido.

Kungiyar Ansar Dine da ake kallon tana da alaqa da kungiyar AlQaida ta lalata wajen bautar musulmai a Tumbuktu, abin da ya janyo kasashen duniya su aka yi tur da al'amarin.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa wajajen bautar da mabiya darikar sufaye ke girmamawa na karfafa bautar gumaka, kuma hakan ya sabawa addinin Musulunci.

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa-da-kasa ta fara bincike na share fage a kan ko aikace-aikacen kungiyar Ansar Dine ya kaiga aikata laifukan yaki.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.