BBC navigation

An zabi sabon shugaban Somalia

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:29 GMT

Sabon shugaban Somalia

Mambobin majalisar dokokin Somalia sun zabi Hassan Sheikh Mahmud a matsayin sabon shugabanksar

Mr Mahmud wanda aka rantsar da shi nan take, malamin jami'a ne mai matsakaicin ra'ayin addinin islama, kuma ya sami rinjayen kuri'un da aka kada, bayan an gudanar da zagaye na biyu na zaben, inda ya doke ShugabanKasar mai ci Sharif Sheikh Ahmed

Bayan gudanar da zagayen farko na zaben dai, sai biyu daga cikin 'yan takarar hudu dake kan gaba suka janye, wadanda suka hada da Fira Minista Abidweli Mohammed

Bayan an sanar da sakamakon zaben dai, an sami rahotannin karar harbe- harben bindiga a matsayin soma shagulgula a birnin Mogadishu

Wannan dai shine zabe na farko a kasar Somalian cikin fiye da shekaru ashirin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.