BBC navigation

9/11: Za a bai wa Amurkawa maganin ciwon daji

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:25 GMT

Ginin da aka kai wa hari a Amurka

Gwamantin Amurka ta ce mutanen da suka tsallake-rijiya-da-baya a lokacin harin da aka kai a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 za su rika karbar magungunan nauo'i hamsin na ciwon daji.

Amurka ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan da aka dauki tsawon lokaci ana kamfe din cewa ya kamata, a bayyana cutar a matsayin wacce ke da alaka da harin na ranar sha daya ga watan Satumba.

A baya gwamnati ta ce ba ta ga wadansu shaidu da ke nuna cewa mutane sun kamu da ciwon ne a lokacin hare-haren ba, sai dai wasu sababbin hujjoji sun sanya ta sauya tunaninta.

Hakan na faruwa ne a yayin da kasar ke bikin zagayowar ranar da aka kai hare-hare akan ginin ma'aikatar tsaron kasar, Pentagon, da kuma tagwayen gine-gine na cibiyar kasuwanci ta duniya da ke birnin New York.

Sun shaki guba

Mutane kusan 3000 ne suka mutu a hare-haren ranar 9 ga watan Satumbar shekarar 2001, kuma akasarinsu sun mutu ne sanadiyar wutar da ta kona su da kuma baraguzan ginin da suka danne su.

Kazakila kusan mutane 1000 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cututtuka bayan hare-haren da aka kai kan tagwayen gine-ginen.

Da dama daga cikin mutanen da suka tsira- wadanda suka hada da 'yan kwana-kwana, da 'yan sanda - sun yi ikirarin cewa wata guba da suka shaka a lokacin da suke aiki a wajen ta sa sun kamu da cutar cancer.

Don haka a yanzu za a sanya mutane kimanin 50 cikin jerin mutanen da ke karbar magani a kyauta sanadiyar hare-haren.

Yawancin mutanen na fama ne da cutukan da suka shafi numfashi da kuma kaduwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.