BBC navigation

'Yan yankin Catalan na Spain na neman 'yanci

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:20 GMT

Masu maci

Mazauna yankin Catalan na Spain su kimanin miliyan daya da rabi suna maci a birnin Barcelona domin neman 'yan cin kai ga yankinsu mai dan kwarya-kwaryan 'yan cin cin gashin kai.

Tsakiyar birnin na Barcelona dai ya cika makil da jamaa, wadanda ke dauke da tutoci masu launin ruwan dorowa da ja, suna rera take mai cewa "Catalonia, wata sabuwar kasar Turai".

Masu aiko rahotanni sun ce, manufar wannan gangami dai shi ne, yin taro mafi girma na neman 'yan cin kan yankin, kuma bisa ga dukkan alamu sun cimma wannan buri na su.

Masu yin macin na kuma neman gwamnatin Spain ta sake duba yarjejeniyar ta da yankin na Catalan akan batun haraji.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.