BBC navigation

'Yan tawayen da Rwanda ke marawa baya sun tafka ta'asa a Congo

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:00 GMT
'Yan tawaye a Congo

'Yan tawayen m23

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Human Rights Watch, ta ce ta na da sabbin shaidu kan irin ta'asar da 'yan tawayen da Rwanda ta marawa baya suka tafka a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Kungiyar ta ce bincike ya nuna cewa kungiyar 'yan tawayen da aka fi sa ni da MR3, sun tilastawa kananan yara maza shiga aikin soji.

Wata jami'a a kungiyar Annak Van da Bag ta shaidawa BBC cewa sun samu bayanai da su ka nuna cewa an hallaka kimanin yara 33 wadanda aka tilastawa shiga aikin soji, bayan sun yi yunkurin tserewa.

Hukumomin kasashen waje dai sun dakatar da kai agaji zuwa kasar ta Rwanda, bayan wani zargi da a ka yi a baya cewa su na marawa 'yan tawayen baya.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.