BBC navigation

Hukumomi a Kenya sun sanya dokar takaita zirga-zirga

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:35 GMT
Wata bukka da aka kona a tashin hankalin Kenya

Wata bukka da aka kona a tashin hankalin Kenya

Ana cigaba da tashin hankali a Tana da ke gabar tekun kasar Kenya, duk da dokar hana zirga-zirga da gwamnatin kasar ta sanya, daga safiya zuwa maraice.

Hakan ya biyo bayan rikicin kabilancin da aka yi da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 112.

Hukumar bada agaji ta Red Cross ta ce wasu karin mutane uku sun rasa rayukan su, ciki har da wani jami'in dan sanda a tashin hankali na baya-bayan nan.

Wasu daruruwan mutane dauke da bindigogi da adduna ne suka kai harin.

An dade ana takaddama tsakanin manoma 'yan Pokomo da kuma makiyayan Orma akan mallakar ruwa da filaye.

Shugaban kasar Mwai Kibaki ya sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin na Tana a ranar litinin da ta gabata.

Wanda ya ke aiko wa BBC rahotanni daga Kenya yace, batun ya zarta gaba tsakanin kabilun biyu da basa ga maciji da juna, akwai gasa a tsakaninsu wajen samun arziki, a kasar da take da matukar nuna banbanci a tsakanin al'umma.

Ya kara da cewa fargabar ita ce, zabukan da za a yi a watan Maris na karatowa a kasar ta Kenya.

Gasar za ta iya ta'azzara tashin hankalin da ka iya kaiwa ga irin wanda kasar ta fuskanta a lokacin zabukan da aka yi a watan Disamba shekarar 2007.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.