BBC navigation

Andy Murray ya lashe gasar US Open

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:53 GMT

Andy Murray da mahaifiyarsa, Judy

Shahararren dan kwallon tennis, Andy Murray, ya lashe wasan karshe na gasar US Open inda ya zama dan Birtaniya na farko a bangaren maza da ya lashe gasar cikin shekaru saba'in da shida.

Bayan da aka sake sanya ranar wasan zuwa ranar Litinin a birnin New York saboda rashin kyawun yanayi, sai da Andy Marray ya shafe kusan sa'o'i biyar kafin ya doke abokin karawarsa dan kasar Serbia, Novak Jokovich, a daya daga cikin wasannin karshe mafiya tsawo da aka taba gani a tarihin gasar.

A watan da ya gabata ne dai dan wasan ya yi nasarar cin lambar zinare a wasan tennis a gasar wasannin Olympics.

Ana sa ran Murray zai karbi kyautar dala miliyan biyu saboda nasarar da ya samu.

Dan Birtaniya na karshe da ya taba lashe gasar shi ne Fred Perry a shekarar 1936.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.