BBC navigation

Har yanzu cutar shan -inna na yaduwa a Najeriya

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:58 GMT
Ana baiwa yara riga kafin Polio

Ana baiwa yara riga kafin Polio

Wani kwamitin kwararru da yayi nazarin a kan yakin da Najeriya ke yi da cutar shan-inna yace, har yanzu cutar na bulla a wasu jihohin da ke arewacin kasar.

Kwamitin ya kuma ce, akwai yiwuwar cutar shan-innar ta yadu zuwa wasu kasashen duniya idan ba a dauki kwararan matakai ba.

Kwamitin dai ya dora alhakin ci gaba da yaduwar cutar ne akan wasu gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, wadanda ya yi zargin cewa, ba sa baiwa gangamin yaki da cutar cikakken goyon baya.

Najeriya dai na daga cikin kasashe uku da suka rage a duniya, wadanda har yanzu ba su yi nasarar kawar da cutar da shan inna ba baki dayanta.

Kwamitin ya tabbatar da cewa a wasu jihohin arewacin Najeriyar su takwas, a halin da ake ciki kimanin mutum saba'in da bakwai ne suka harbu da cutar.

Wannan na faruwa, inji kwamitin, a daidai lokacin da kusan dukkan kasashen duniya suka ci yakin da ake yi da cutar, in ban da kasashen Pakistan da Afganistan.

Haka kuma Kwamitin ya bayyana cewa akwai matsaloli da dama da ke janyo cikas a yakin da ake yi da cutar a Najeriya.

Ya ce, daga ciki har da tirjiyar da iyaye ke yi wajen ba da 'ya'yansu domin a yi musu riga-kafi.

Bugu da kari kuma kwamitin ya ce, rikice-rikicen da ake fama da su, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma rashin cikakken goyon baya daga wasu gwamnatocin jiohohi da kananan hukumomi na taimakawa ga kasa cimma yakin da ake yi da cutar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.