BBC navigation

David Cameron ya amince da zaben Shugaban Kasar Somalia

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:29 GMT
Hassan Sheikh Mohamud

David Cameron ya amince da zaben Hassan Sheikh Mohamud

Fira Ministan Burtaniya , David Cameron, ya yi na'am da zaben sabon shugaban Kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud.

Mr. Cameron din ya ce wannan wani lokaci ne mai muhimmanci, kana kuma muhimmin mataki da zai kai ga ci gaban sabon tsarin tafarkin dimokaradiyya.

Sai dai kungiyar nan mai zazzafan ra'ayin addinin Islama ta al Shabab, da har yanzu ke rike da ikon wasu daga cikin yankunan dake arewacin kasar sun yi allawadai da zaben.

Sabon shugaban Hassan Sheikh Mohamud wanda ya samu galaba kan shugaba mai ci, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, ya mika godiyarsa ga majalisa, kana ya yi alkawarin jagorantar kasar yadda ya kamata.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.