BBC navigation

Musulmi sun gudanar da zanga zangar lumana a Jos

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:23 GMT
Najeriya

Musulmi sun gudanar da zanga zanga a Jos

Rahotanni daga Najeriya na cewa dazu da yamma ne wasu musulmi a Jos, babban birnin jahar filato su ka gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu game da fim din nan da aka yi a Amurka dake nuna wani Mutum a matsayin Annabi Mummad Sallallahu Alaihi Wa Sallam

Masu zanga zangar dai sun daga kwalaye sama wadanda ke dauke da rubutu na yin tir da Kasashen Amurka da Isra'ila

An dai gudanar da zanga-zangar cikin lumana a birnin na Jos.

Daga baya dai jami'an 'yansanda sun dakatar da masu zanga zangar.

Musulmi a sassa daban-daban na duniya dai sun gudanar da zanga zanga makamanciyar wannan, domin nuna bacin ransu game da wannan batu.

Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta umurci jami'anta da ke kasar baki daya da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.